Home Labarai Shin ko murabus din Badaru ya yi zai kawo karshen matsalar Tsaro...

Shin ko murabus din Badaru ya yi zai kawo karshen matsalar Tsaro a Najeriya

94
0

Ministan tsaron Najeriya, Mohammad Badaru Abubakar, ya ajiye muƙaminsa a yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar matsananciyar matsalar tsaro.

A cewar wata sanarwa da mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar da daren Litinin, Badaru ya mika takardar murabus dinsa ga Shugaba Bola Tinubu. Sanarwar ta ce shugaban ƙasar ya amince da murabus din tare da gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake rike da muƙamin.

Murabus ɗin na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar karin tabarbarewar tsaro, musamman a yankunan arewa. Satar dalibai 25 a jihar Kebbi da kusan mutane 300 a jihar Neja na daga cikin manyan al’amuran da suka tsananta damuwa kan tsaron ƙasa.

Haka kuma, harin da aka kai wa masu ibada a wani coci a jihar Kwara, tare da sauran hare-hare da satar mutane a jihar Kogi, sun ci gaba da jaddada kalubalen da gwamnatin tarayya ke fuskanta wajen yaki da rashin tsaro.

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa dalilin da ya sa Badaru ya ajiye aiki ya shafi lafiyarsa.

Duk da haka, a lokacin da Badaru yake jagorantar ma’aikatar tsaro, hare-haren Boko Haram a arewa maso gabas da kuma na ’yan bindiga a arewa maso yamma sun ci gaba da faruwa.

A wata tattaunawa da BBC cikin makon da ya gabata, Badaru ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na yin duk mai yiwuwa don magance matsalar tsaro. Ya ce ana ci gaba da bincike domin gano musabbabin dawowar satar ɗalibai a makarantu.

> “Ina tabbatar maka cewa sojojinmu na aiki ba dare ba rana domin kawar da wannan barazana,” in ji shi.

Wane ne Mohammad Badaru Abubakar?

Mohammad Badaru Abubakar tsohon gwamnan jihar Jigawa ne, inda ya shugabanci jihar daga 2015 zuwa 2023.

Ya zama Ministan Tsaro ne bayan nadin Shugaba Tinubu a watan Agusta 2023.

Ya kammala karatun ilimin akanta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Ya halarci cibiyar horaswa kan manufofi da tsare-tsare a Jos, jihar Filato.

Fitaccen ɗan kasuwa ne, ya rike mukamai a manyan ƙungiyoyin kasuwanci a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 7   +   5   =