Home Siyasa Alamu Sun Nuna Yiwuwar Ficewar Gwamna Abba Kabir Daga NNPP Zuwa...

Alamu Sun Nuna Yiwuwar Ficewar Gwamna Abba Kabir Daga NNPP Zuwa APC

111
0

Biyo bayan rade radin ficewar gwamna Abba Kabir Yusif daga jamiyyar NNPP zuwa APC da aka fara makon jiya, yanzu haka a iya cewa lamarin na gab da tabbata.

Gwamna Agbu Kefas Zai koma Jam’iyyar APC – Shugaban Jam’iyyar Taraba

Jam’iyyar APC a Zamfara ta sake jaddada goyon bayanta ga Shugaba Tinubu a 2027

Yan Majalisar Dokoki biyu na jihar Zamfara sun fice daga Jam’iyyar APC

A karshen makon nan ne aka jiyo wasu jiga jigai a fadar Gwamnati Kano da suka hada da babban hadimi da kan shirye aikace aikacen gwamnan Abdullahi Ibrahim Rogo da Daraktan yada labaran Gwamna Sanusi Bature Dawakin Tofa wajen wani taro a yankunansu, da aka ce na tattauna sahalewa gwamna Abba Kabir Yusif ya koma jamiyyar APC mai mulki ne.

An jiyo Rogo na cewa masu ruwa da tsaki a karamar hukumar da suka hada da shugaban majalisar dokokin Kano, Jibril Isma’il Falgore sun amince gwamnan ya sauya sheka zuwa APC

Shima takwaransa Sanusi Bature Dawakin Tofa, Kakakin gwamna Kano yayi irin wannan furuci, a taron masu ruwa da tsaki na jamiyyar NNPP a karamar hukumar Dawakin Tofa, a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na facebook.

Masana siyasa na kallon fara shirya irin wadannan taruka kamar sharar fage ne na ficewar gwamnan da mukarrabansa zuwa jamiyyar APC mai mulki, wanda hakan zai bude sabon shafi a fagen siyasar jihar Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 0   +   5   =