Amurka ta yi barazanar saka takunkumai da hana bizar shiga ƙasarta ga duk wanda ta samu da hannu a zargin yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya.
Ministan harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ne ya wallafa hakan a shafinsa na X
“Matakin, martani ne ga matsalar yi wa Kiristoci kisan gilla, zargin da bai bayar da wata hujja a kansa ba”. In ji Ministan.
A jiya Laraba ne wani kwamatin Majalisar Wakilan Amurka ya fitar da rahoto kan zargin, inda wasu ‘yanmajalisa suka nanata iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci da gangan a Najeriya.
Najeriya dai ta sha musanta batun yiwa kiristoci kisan kiyashi, inda ta ce masu yada wannan Magana na son tada zaune ne kawai, tare da yi wa kasar nan makarkashiya.








