Shekarar 2026 shekara ce da Najeriya za ta fuskanci manyan al’amura masu ɗaukar hankali.
Irin abubuwan da ake tunani zasu faru a 2026 a bangaren siyasa da tatta
INEC za ta gana bangarorin dake rikici a jam’iyyar ta PDP
Alamu Sun Nuna Yiwuwar Ficewar Gwamna Abba Kabir Daga NNPP Zuwa APC
Kama daga na siyasa da tattalin arziki, da sauran fannonin rayuwar ƴan ƙasar da dama.
A fagen siyasar ƙasar ana ra ran ganin abubuwa da dama kama daga kaɗa kugen babban zaɓen ƙasar na baɗi zuwa tsayar da ƴan takara da sauran abubuwa.
Dokta Yakubu Haruna Ja’e shugaban Malami a jami’ar jihar Kaduna ya ce gaba-ɗayan wannan shekara za ta karkata ne kan al’amuran siyasa a Najeriya, ”ta yadda in ba a yi hankali ba duka zaɓaɓɓu za su mayar da hankali kan yaƙin neman zaɓe maimakon aiki”.
Cikin wannan muƙala mun rairayo wasu daga cikin abubuwa na siyasa da ake sa ran faruwarsu a Najeriya cikin wannan sabuwar shekara ta 2026.









