Home Tsaro Yan sandan jihar Kano sun kama matasa da ake zargi da addabar...

Yan sandan jihar Kano sun kama matasa da ake zargi da addabar unguwannin Medile da Guringawa

101
0

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wasu matasa da ake zargi da addabar unguwannin Medile da kuma Guringawa da fashi da makami, inda su ke haurawa gidajen mutane.

Rundunar ‘Yan Sanda:Mun Tsaurara Tsaro A Kan Iyayokin Kano

Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya ta kama Alwan Hassan

‘Yanbindigar Da ke Addabar Kano Daga Jihar Katsina Suke – Gwamnan Kano

Kakakin ƴan sandan Kano CSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a tattaunawar da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kiyawa ya ce Wasu mazauna unguwannin da aka shiga gidajensu sun bayyana yadda matasan suka riƙa ɓalle ƙofafen gidajensu suna sanya musu wuƙa a wuya, har ma suka yi wa wasu rauni.

CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa ana ci gaba da gudunar da bincike akan wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar yan sandan Kano dake Bampai.

Daga bisani rundunar yan sandan jihar Kano tace da zarar an kammala bincike kan matasan za’a gudunar dasu a gaban kotu domin fara fuskantar shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 10   +   2   =