Home Tsaro Yaki da Boko Haram ya wuce yaƙin Basasa-Obasanjo

Yaki da Boko Haram ya wuce yaƙin Basasa-Obasanjo

32
0

Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa yaki da ‘yan Boko Haram a Najeriya ya ɗauki tsawon lokaci fiye da Yaƙin Basasa na 1967–1970.

Obasanjo ya yi wannan tsokaci ne a ranar Lahadi a wani shirin talabijin, wanda Bishop Matthew Kukah da tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Kingsley Moghalu suka halarta.

Ya ce dakile ‘yan ta’adda na bukatar haɗin dabaru na musamman, kayan aiki na zamani, bayanai masu inganci, da fasahar zamani.

Obasanjo ya bayyana cewa babu laifi sojojin Najeriya su samu horo daga ƙasashen da suka yi nasara wajen yaki da ‘yan ta’adda, inda ya kawo Colombia a matsayin misali.

Ya jaddada cewa horon yau da kullum bai isa wajen tunkarar ‘yan ta’addan da suke yawo ko shiga cikin jama’a ba.

Tsohon shugaban ya yi gargadi cewa rashin kyakkyawar hanyar siyan kayan yaki da musayar bayanai zai iya kawo koma baya a yaki da ‘yan ta’adda.

Ya ce bai kamata a bar sojoji su kadai su sayi kayan yaki ba, domin harkar ta zama kamar masana’antu.

Daga kwarewarsa wajen yaki da masu tada zaune tsaye a Niger Delta, ya bayyana cewa ba za a iya kawar da yiwuwar haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da ‘yan ta’adda ba.

Obasanjo ya kara da cewa ya ziyarci Maiduguri a 2011 domin fahimtar asali, koke-koke da tsarin shugabancin Boko Haram.

Ya kuma bayyana cewa a farko ‘yan ta’addan sun ƙi tattaunawa da Gwamnatin Tarayya, kafin daga bisani su amince da tsagaita wuta na kwanaki 21, wanda bai yi tasiri ba saboda rashin kyakkyawar tattaunawa da shugabanninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 5   +   9   =