Home Labarai Gwamnatin Kano ta ƙara jaddada haramcin sana’ar Achaba

Gwamnatin Kano ta ƙara jaddada haramcin sana’ar Achaba

93
0

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da jaddada aiwatar da dokar hana sana’ar achaɓa ta shekarar 2013, wani mataki da ta ce zai taimaka wajen kare tsaro da rage laifuka, da tabbatar da doka da oda a fadin jihar.

Ma’aikatar Shari’a ta bayyana cewa dokar, wadda ta dade tana nan daram kuma za a ci gaba da aiwatar da ita sosai.

Babban lauyan jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya buƙaci jama’a musamman masu baburan haya wata acaɓa da su yi biyayya ga tanade-tanaden dokar.

A cewarsa, gwamnatin jihar ba za ta lamunci karya dokar ba, musamman a yankunan da aka haramta acaɓa.

Dokar ta hana achaɓa a cikin wasu muhimman ƙananan hukumomin birnin da suka haɗa da Kano Municipal, Gwale, Dala, Nassarawa, Tarauni, Ungogo (Jido), Dawakin Kudu (Tamburawa, Gurjiya da Jido Ward), Fagge da Kumbotso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 7   +   3   =