Home Labarai Gwamnatin Nasarawa za ta kafa yan sandan Jiha

Gwamnatin Nasarawa za ta kafa yan sandan Jiha

90
0

Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana cewa tana da shirin kafa rundunar ’yan sandan jiha, muddin gwamnatin tarayya ta amince da sauye-sauyen kundin tsarin mulki da ake tattaunawa a kansu.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, CP Usman Baba, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Lafia. Ya ce tun bayan hawar gwamnatin Abdullahi Sule a 2019, an mayar da hankali sosai kan inganta tsaro ta hanyar tallafa wa hukumomin tsaro da motocin aiki, kayan fasaha da sauran muhimman kayayyaki.

Ya tabbatar da cewa gwamna Sule na da yaƙinin ganin jihar ta kasance cikin kwanciyar hankali da ta dace ga masu zuba jari da kuma al’ummar jihar gaba ɗaya. Don haka ne ake ci gaba da tura jami’an tsaro zuwa makarantu a yankunan da ake zargin barazana, tare da manyan wuraren ibada a Lafia da sauran ƙananan hukumomi 13.

Dangane da yawaitar garkuwa da mutane, kwamishinan ya ce gwamnatin jihar na aiki kafaɗa-da-kaɗe da jami’an tsaro, ’yan sa kai da masu sa ido a unguwanni domin dakile lamarin. Ya kuma gargadi masu aikata laifuka da cewa Nasarawa za ta zama “wuri mai zafi” gare su, domin duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsauri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 9   +   5   =