Babbar Kotun Tarayya a Najeriya ta bayar da umarni ga jam’iyyar adawa ta PDP da ta ba wa tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, damar shiga takarar shugabancin jam’iyyar.
Rahotanni sun bayyana cewa Mai Shari’a Peter Odo Lifu ya ce kuskure ne matakin da PDP ta ɗauka na hana Lamido sayen fom ɗin takara.
Kotun ta kuma dakatar da babban taron jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, tana mai cewa PDP ta gaza bin ka’ida wajen wallafa jadawalin taron a kan lokaci domin sanar da mambobinta, kamar yadda dokar zaɓe ta tanada.
Wannan shi ne karo na uku da kotu ke bayar da umarni da ya shafi dakatar da taron da PDP ke shirin gudanarwa domin zaben sabbin shugabanni na ƙasa.
Sai dai jam’iyyar, ƙarƙashin jagorancin Umar Ilya Damagum, ta bayyana cewa za ta ci gaba da shirye-shirye, tana mai cewa ita ma tana da wani umarnin kotu da ya ba ta damar gudanar da taron kamar yadda aka tsara.









