Home Labarai Sarkin Musulmi Ya Yaba wa Sojoji kan tsoro

Sarkin Musulmi Ya Yaba wa Sojoji kan tsoro

22
0

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar III ya yaba wa sojojin Najeriya bisa jajircewarsu wajen kare rayuka da kuma dukiyoyin ƴan Najeriya.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin hafsan sojojin ƙasa, Laftanar-Janar Waidi Shaibu a fadarsa da ke Sokoto ranar Juma’a, 26 ga Disamban, 2025.

Yayin ziyarar, Janar Shaibu ya ƙara tabbatar da zimmar sojojin ƙasar wajen ƙarfafa aiki da al’umma da kuma haɗin-kai da sarakuna don ganin an samar da zaman lafiya da tsaro.

Sultan Abubakar ya kuma yi addu’ar cewa Allah ya ci gaba da bai wa sojojin nasara a dukkan ayyukansu na kare ƴan ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 4   +   7   =