Home Tsaro Safarar Yara: Gwamnatin kogi ta ceto yara 21

Safarar Yara: Gwamnatin kogi ta ceto yara 21

36
0

Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana cewa jami’an tsaro sun ceto yara 21 masu shekaru 6 zuwa 17 da ake zargin an yi safarar su.

Safarar Yara: Gwamnatin kogi ta ceto yara 21

NAPTIP A Kano Ta Kama Mai Tura Mata Aikatau Zuwa Saudiyya

Yan Sanda Sun Ceto Yara 17, tare da Cafke waɗanda ake Zargin da Safarar su

A cewar sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya fitar a ranar Litinin, 8 ga Disamba, jami’an NSCDC tare da wasu jami’an tsaro sun tsaya wata mota da misalin ƙarfe 3 na rana, inda aka tarar da yaran a cikinta ba tare da cikakkiyar hujja daga mutanen da ke tare da su ba.

Binciken farko ya nuna cewa an tattaro yaran ne daga jihohin Arewa daban-daban, ba tare da sahihin bayanin inda za a kai su ba.

Sanarwar ta ce an kama wasu mutane da ake zargi da hannu a safarar, ciki har da waɗanda suka ce za su kai yaran wata makarantar allo a Yagba East.

Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Ahmed Ododo ya umurci Ma’aikatar Kula da Harkokin Mata ta jihar da ta karɓi yaran, ta basu kulawa da tallafi domin kwantar musu da hankali.

Sanarwar ta kara da cewa ana ci gaba da bincike, kuma duk wanda aka tabbatar da hannu a safarar yaran za a gurfanar da shi bisa dokokin jihar kan safarar yara da kare hakkin yara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 10   +   7   =