Idan ganga ta fiye zaƙi fashewa ta ke, Ndume ya gargaɗi APC akan guguwar sauyin sheƙa zuwa cikin ta
Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu, ya ce jam’iyyar APC na fuskantar barazana saboda yawaitar ’yan siyasa masu sauya sheka zuwa jam’iyyar.
Yayin jawabi a taron Nnamdi Azikiwe Award Lecture da aka yi a Abuja, Ndume ya ce ko da yake shugabannin jam’iyyar na buɗe ƙofa ga waɗanda suka bar jam’iyyunsu, hakan na iya zama nauyi da ka iya “kifewar jam’iyyar kamar jirgi da ya cika da kaya marasa nauyi.”
Ndume ya roki ’yan siyasa su haɗa kai da Shugaba Bola Tinubu domin ci gaban kasa, yana mai cewa jam’iyyun adawa suna mai da hankali ne kan zaben 2027 maimakon su ba da gudummawa ga mulki.
A nasa bangaren, Mu’azu Aliyu, tsohon gwamnan Neja, ya yi gargadin cewa yawaitar sauya sheka zuwa APC na barazanar mayar da Najeriya jam’iyya ɗaya, yana mai cewa PDP ta “cire cutar da ta tabarbare ta” domin farfado da jam’iyyar.









