Idan ba a samu wani sauyi na ƙarshe ba, Shugaba Bola Tinubu zai naɗa tsohon Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa, domin ya maye gurbin Badaru Abubakar a matsayin ministan tsaro.
Badaru Abubakar ya yi murabus daga mukaminsa na ministan tsaro a ranar Litinin, inda ya danganta hakan da dalilai na lafiya.
Majiyoyi masu tushe da suka san da lamarin sun shaida wa wakilinmu cewa Shugaba Tinubu ya kammala shirye-shiryen naɗa Mista Musa domin ya maye gurbin Badaru Abubakar, bayan matsin lamba daga cikin gida na ganin an saka tsohon jami’in soja a majalisar zartarwarsa.
DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa tsohon babban hafsan tsaron ya gana da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa a daren Litinin.
Wakilin jaridar The Punch ya ga Mista Musa yana isa Fadar Ƙasa da ƙarfe 7:03 na yamma a ranar Litinin, inda wani babban jami’in tsaro ya jagorance shi zuwa ofishin Shugaban Ƙasa.








