Home Labarai Jami’an Tsaro suyi aikisu ba tare jiran umarni ba ~ Christopher Musa

Jami’an Tsaro suyi aikisu ba tare jiran umarni ba ~ Christopher Musa

170
0

Sabon Ministan Tsaro Janar Christopher Musa ya umarci jami’an tsaro da su gudanar da aikin su batare da jiran umarni ba.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya umurci ma’aikatan ma’aikatar, na soja da farar hula, da su zage dantse kuma su ƙara ƙoƙari wajen aiki ba tare da jiran umarni ba.

Musa ya faɗi haka a lokacin da ya shiga ofishinsa a hedikwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja a ranar Juma’a. Ya yi alƙawarin zai jagoranci ba tare da ɓata lokaci ba, da rikon amanar da aka ba shi.

Musa, wanda a baya ya kasance shugaban hafsoshin soji, ya ce yana dawowa ma’aikatar ne da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da kuma amincewar jama’ar Najeriya. “Bayan shekara 39 a aikin soja, yanzu na zo na zama Ministan Tsaro, soyayyar da Nijeriya ta nuna mana ta nuna cewa mutane sun yi imani za mu iya juyar da al’amura na tabarbarewar tsaro. “Zubar da jinin marasa laifi ya zo ƙarshe. ’Yan ƙasa suna da haƙƙin rayuwa ba tare da tsoro ba. Yara su koma makaranta. Manoma su koma gonakinsu,” in ji shi.

Musa ya ba da tabbacin cewa jin daɗin ma’aikatan soji da iyalansu shine jigon dawo da amincewar jama’a da ingantaccen aiki. A cewarsa, duk wanda ke ba da ransa domin ƙasarsa ya cancanci a ba shi mafi girman girmamawa. Ya yi alƙawarin ma’aikatar za ta yi gaggawar tabbatar da cewa sojoji sun samu kayan aiki da ake bukata, biyan kuɗin aiki da lokaci, gidaje masu kyau da kula da lafiya, musamman ga waɗanda suka ji rauni da iyalan waɗanda suka rasu.

Daga karshe Ministan yayi fatan haɗa karfi da karfe domin kawo canji a fannin tsaro na ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 7   +   8   =