Rundunar yan’sanda tabbatar da kai hari makarantar sakandare ta gwamnati Girls Comprehensive Senior Secondary School mega a jihar Kebbi.
Gidan jaridar Daily Trust ta rawaito cewa yan’bindigar sun afka makarantar kwana ta ɗaliban mata, inda suka dauke daliban 25 tare da kashe mataimakin shugaban makarantar.
Mai magana da yawun yan’sanda na jihar CSP Nafi’u Abubakar yace ” Bamu samu rahoto ba ko kira ba lokacin faruwar lamarin.
Csp Nafi’u ya kara da cewa yan bindiga sun zo ne dauke da manyan bindigogi, haka zalika lokacin da suka zo kofar makarantar a rufe take, amma duk da haka sun kutsa cikin makarantar, sun kuma dauke daliban mata guda 25.
Ya kara da cewa ƙwararrun jami’an su sun zage gurin da abun ya faru, amma tuni yan’bindigar sun dauke daliban.
Mataimakin gwamna jihar umar tafida tare da Sakataren Gwamnatin, sun ziyarci makarantar bayan faruwar lamarin, yayin da gwamnan jihar Ahmad Idris yayi tafiya wajen kasar.
Wani wada ya faɗi yanda abun ya faru, wanda shi mazauni ne a yankin gurin mai suna Aliyu Yakubu ya ce yan’bindigar sun zo ne da misalin ƙarfe 5 na safe na yau ranar Litinin, kuma basu iske kowa ba a bakin ƙofar makarantar.
Inda ya kara da cewa sun harbi shugaban makarantar ne sakamakon yayi kokarin kare daliban lokacin da zasu tafi da daliban, inda ya kara da cewa wannan abun takaici da koma baya a cikin ilahirin wajan.









