Home Labarai Amnesty International ta yi Allah-wadai da garkuwa da mata sama da 25...

Amnesty International ta yi Allah-wadai da garkuwa da mata sama da 25 da ‘yanbindigar suka yi

243
0

Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da garkuwa da mata sama da 25 da aka yi a makarantar sakandare ta mata da ke garin Maga a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ƙungiyar ta bayyana da abin ban mamaki.

Ƙungiyar ta ce sace matan na ƙara nuna gazawar gwamnatin Najeriya wajen kare rayukan al’ummar ƙasar da dukiyoyinsu.

“Bincikenmu ya gano cewa an sace matan ne bayan ƴanbindiga sun kutsa makarantar da misalin ƙarfe 5 na safiya, inda suka kashe mai gadi, da mataimakin shugaban makaranta, sannan suka tilasta wani ya nuna ɗakin kwanan ɗalibai mata, inda suka yi awon gaba da ɗaliban.”

Ƙungiyar ta ce wannan sace ɗaliban na nuna cewa “gwamnatin Tinubu ba ta da wani tsari ingantacce na kawo ƙarshen ta’addancin ƴanbindiga da suka ɗauki shekaru suna yi aika-aika a ƙasar, domin wannan na nuna cewa dukan matakan da gwamnatin ta ɗauka ba sa aiki domin ba a sa haifar da ɗa mai ido,” kamar yadda ƙungiyar ta bayyana a wata sanarwa.

Amnesty ta buƙaci gwamnatin ta ɗauki matakin gaggawa wajen ceto ɗaliban, sannan ta buƙaci hukumomi a ƙasar su gudanar da bincike domin ganowa tare da kare yawaitar sace-sacen mutane a jihar, wanda a cewarta yake barazana ga ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 5   +   6   =