Fitaccen malamin addini, Dr. Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana wannan ra’ayi ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Ya ce tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya fahimci muhimmancin wannan hanya tun lokacin da yake kan mulki a jihar.
A cewarsa, Matawalle ya fifita kare rayukan fararen hula, inda ya rungumi hanyar sasanci da tuntuba da ɓangarorin da ke rikici. Wannan mataki, a cewar Gumi, ya taimaka wajen rage ayyukan ta’addanci a wasu yankuna, lamarin da ya sa zirga-zirga da harkokin kasuwanci suka fara dawowa daidai.
Sai dai Gumi ya nuna cewa rashin cikakken goyon baya da daidaito daga wasu sassan tsaro ya sake janyo tabarbarewar tsaro a wasu wurare.
Yanzu da Matawalle ke rike da mukamin Ministan Tsaro, Gumi ya ce yana amfani da gogewarsa wajen lalubo hanyoyin da za su haifar da zaman lafiya mai ɗorewa, inda gwamnati ke fatan wannan salo zai taimaka wajen tabbatar da tsaro, hadin kai da ci gaban kasa.








