Hukumar zabe mai zamanm kanta ta reshan jihar kano tace ta samar da wata sabuwar manhaja wadda zata bawa yan kasa damar yin rijistar katin zabe a duk lokacin da suke da bukata.
Jami’in wayar da kan jama’a akan zabe na hukumar zabe mai zaman kan ta reshen jihar Kano, Garba Ashiru ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Premier radio.
Ya kara da cewa, samar da sabuwar manhajar zata taimaka wajan rage cinkoson da ake samu a wuraran da ake yin rijistan katin zaba.
Garba Ashiru yana mai bayyana cewa, tuni aka fara baje kolin sunayen wadanda suka yi rijistan katin zaban a baya a daukacin kananan hukumomi 44.
Daga bisani hukumar zaban mai zaman kan ta kasa reshen jihar Kano ta tabbatar da cewa, zata ci gaba da yin aiki tukuru domin ganin an samu nasarar shirin da aka sanya a gaba.









