Home Siyasa Tinubu Ya Yi Alkawarin Ci Gaba da Ayyukan Buhari

Tinubu Ya Yi Alkawarin Ci Gaba da Ayyukan Buhari

92
0

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ayyuka da manufofin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, inda zai ɗora a kan inda marigayi ya tsaya.

EFCC ta tsare tsohon ministan ƙwadago, Chris Ngige

An sake nada Buba Marwa a matsayin Shugaban NDLEA

Ba ma amfani da EFCC Wajen Cin Zarafin ’Yan Adawa – Gwamnatin Tarayya

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja, yayin da ya ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Buhari wanda Dr. Charles Omole ya rubuta.

Shugaban ƙasar ya ce mafi girman girmamawa da za a yi wa Buhari ita ce ci gaba da ayyukan shugabancinsa, daga inda ya tsaya.

Ya kuma bayyana cewa littafin ya nuna tarihin Buhari cikin adalci, yana bayyana nasarori da kura-kurai, tare da ƙarfafa shugabanni na gaba su koyi darussa daga rayuwarsa.

Tinubu ya kuma waiwayi doguwar tafiyarsa ta siyasa tare da Buhari, inda ya bayyana shi a matsayin “ɗan’uwa, aboki da abokin tafiya a siyasa.”

Marubucin littafin, Dr. Charles Omole, ya ce littafin ya tattaro tarihin rayuwar Buhari tun daga haihuwa har zuwa rasuwarsa, tare da shaidu daga mutanen da suka yi aiki tare da shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 2   +   9   =