Home Tsaro Gwamnatin tarayya za ta fara sabbin dokokin haraji daga 1 ga wata...

Gwamnatin tarayya za ta fara sabbin dokokin haraji daga 1 ga wata janairu,2026.

23
0

Gwamnatin ta  ce an yi gyaran ne domin bunƙasa tattalin arziƙi da rage wa ’yan Najeriya wahalhalu.

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele ne, ya faɗi haka bayan ya gabatar wa Shugaba Bola Tinubu rahoto a Legas.

Ya ce an riga an fara aiwatar da dokoki biyu daga cikin huɗu, yayin da sauran biyun za su fara aiki a watan Janairu.

“Shirin fara aiwatar da sabbin dokokin haraji daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026 zai tabbata kamar yadda aka tsara,” in ji Oyedele.

“Waɗannan gyare-gyare an yi su ne domin samar wa ’yan Najeriya sauƙi.”
Oyedele, ya bayyana cewa gwamnati ta shafe watanni tana shirin fara aiwatar da dokokin ta hanyar horaswa, tsare-tsare da wayar da kan jama’a.

Ya ƙara da cewa manufar gyaran ba wai tara kuɗi ba ne.
“Wannan gyara na nufin bunƙasa tattalin arziƙi da tabbatar da adalci,” in ji shi.

“Idan mutane da dama sun shiga tsarin biyan haraji, bin doka zai ƙaru kuma kowa zai amfana.”
Gwamnatin ta kuma ce a shirye ta ke ta yi aiki tare da Majalisar Dokoki kan duk wata matsala da ta shafi sabbin dokokin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 1   +   1   =