Home Labarai Duk lokacin da na ji labarin cewa an kashe mutum, sai nayi...

Duk lokacin da na ji labarin cewa an kashe mutum, sai nayi kuka ~ Akpabio

211
0

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya ce alhakin gwmanati ne maido da zaman lafiya da haɗin kai a jihar Filato.

Yayin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar ranar Asabar a birnin Jos, Akpabio ya ce babu wani daga waje da zai kawo wa ƙasar zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shugaban majalisar dattawan na kira ga ƴan Najeriya su zaman to masu zaman lafiya.

Ya kuma jaddada cewa shugaban ƙasa ya shirya tsaf domin magance matsalar tsaro a faɗin ƙasar.

“Ina tsaye a nan domin wakiltar shugaban ƙasa, tare da tabbatar muke cewa zai yi duk mai yiwuwa domin samar da zaman lafiya, ba wasu mutane daga wajen ƙasarmu ne za su zo domin kawo mana zaman lafiya ba, mu ne za mu samar wa kanmu”, in ji shi.

“Ina mai tabbatar wa da ƴan Filato cewa za mu warware muku matsalolinku. Nakan yi kuka a duk lokacin da na ji labarin cewa an kashe mutum, babba ko ƙarami”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 10   +   3   =