Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar bilAdama wadanda aka ceto yara 17 daga hannunsu a garin Zariya.
Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ta bayyana cewa yaran da aka ceto ana zargin an shirya safarar su ne zuwa Abuja da wasu sassan ƙasar da ma ƙetare.
A cewar yan sanda waɗanda ake zargin sun haɗa da Musa Shu’aibu, mai shekara 21 daga Funtua, Jihar Katsina; Sani Mamman, mai shekara 23 daga Ingawa, Jihar Katsina; da Mubarak Ismail, mai shekara 20 daga Unguwa Uku ta Jihar Kano.
Kakakin ya ce, yayin bincike waɗanda ake zargin sun amsa cewa su ne suka tattaro yaran daga wurare daban-daban da zummar kai su Abuja kafin jami’an ’yan sanda su damƙe su.
DSP Hassan ya ƙara da cewa, yaran duk ƙanana ne, kuma suna cikin ƙoshin lafiya da yanzu haka suna hannun rundunar, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano iyayensu ko masu kula da su.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya yaba da bajintar jami’an sashen DanMagaji, inda ya nanata cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani nau’in safarar yara ko cin zarafin su ba.








