Home Labarai Ƴansandan Legas Sun Kama Mutum Biyar Bisa Zargin Shirya Garkuwa ta Ƙarya...

Ƴansandan Legas Sun Kama Mutum Biyar Bisa Zargin Shirya Garkuwa ta Ƙarya Don Yaudarar Iyayen Ɗalibi

24
0

Rundunar ƴansandan Jihar Legas ta kama mutum biyar da ake zargi da shirya garkuwa da mutane na ƙarya, lamarin da ya shafi wani ɗalibi ɗan makaranta da abokansa huɗu domin yaudara da karɓar kuɗi daga iyayensa.

An kama waɗanda ake zargin ne a ranakun 17 da 18 ga Disambar 2025, bayan wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta inda aka ga yaron yana roƙon a tausaya masa, kamar yana cikin maɓoyar masu garkuwa da mutane kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Abimbola Adebisi, ta fitar ranar Juma’a, ta ce binciken farko ya nuna cewa lamarin, wanda ya tayar da hankalin jama’a, an fara kai rahotonsa ga ƴansanda a matsayin ɓatan mutum a ranar 26 ga Nuwamba, 2025.

Ta ƙara da cewa daga bisani bincike ya tabbatar da cewa garkuwar da ake iƙirari, yaron da abokansa ne suka shirya inda suka yi amfani da ɗakin ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin wajen aiwatar da wannan shiri.

Ƴansandan sun kama su ne a yankin Volkswagen Roundabout da kuma Ago Palace a jihar Legas.

Masu bincike sun ce waɗanda ake zargin sun shirya garkuwa da yaron ne domin karɓar kuɗi daga mahaifiyarsa mai suna Aligwo, wadda ta karɓi naira miliyan huɗu kwanan nan daga wata gudummawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 7   +   7   =