Yayin da zarge zarge ke ƙara ƙarfi kan Ƙaramin Ministan Tsaron Nijeriya, Bello Matawalle, ministan ya fito fili ya sanar da cewa duk mai zarginsa da wani lefi da ya je kotu domin kalubalantarsa.
Ministan ya kuma ce idan kotu ba ta same shi da laifi ba duk abin da ya buƙata a biya shi a matsayin bata suna sai an biya shi.
Wannan na zuwa ne yayin da ake wasu daga cikin yan kasar nan ke cigaba da kiraye kirayen da ya sauka daga kan mukaminsa domin a gudanar da bincike.
Matawalle a wata hira da kafar yada labarai ta DCL ta yi a karshen makon nan, ya kuma kara da cewa kiraye kirayen da ake cigaba da yi domin ya sauka na da alaka da binciken da ake cigaba da yi dan gane da yunkurin kifar da gwamanti da aka yi a baya wanda yace ko baya nan za’a cigaba da wannan binciken.
Ya kuma kara da cewa duk zarge zargen da ake masa na da alaka da siyasa wanda tuni gwamanti ta riga da ta wanke shi.
Har yanzu dai gwamnati ba ta ce komai ba game da zargr zargen da ake cigaba da yi akan karamin ministan na zargin alaka da yan fashin daji.








