A garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, jam’iyyar APC ta sake tabbatar da cewa za ta goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Wannan sanarwa ta fito ne a wani babban taro da aka gudanar a yau Juma’a, 14 ga Nuwamba 2025.
Taron ya ci gaba da nuna matsayar da aka cimma a taron farko ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, inda tsohon gwamna Sanata Abdulaziz Yari ya jagoranta.
A yau kuma, Ministan Tsaro Dr. Bello Muhammad Matawalle – wanda aka fi sani da Barden Kasar Hausa – shi ne ya jagoranci taron a ofishin jam’iyyar. Daga mazabu 147 da kananan hukumomi 14, shugabanni da jiga-jigan jam’iyyar sun hallara, suka ce: “Za mu tsaya tsayin daka da Tinubu!” Tsohon gwamna Alhaji Mamuda Aliyu Shinkafi ya ce: “Shugaba Tinubu yana da shirye-shirye masu kyau ga Zamfara, musamman da albarkatun ƙasa da Allah ya baiwa jihar.
Gyare-gyaren da ya yi a tattalin arziki, da kuma burin sa na mayar da Nijeriya ƙasa mai tattalin arziki na dala tiriliyan ɗaya – saboda haka muna goyon bayansa sosai domin ajandar *Renewed Hope*.” Tsohon mataimakin gwamna Malam Ibrahim Wakkala ya yi kira: “Yari da Matawalle su kasance kamar ’yan biyu, su haɗa kan ’yan jam’iyya, domin haɗin kai shi ne abin da ya fi muhimmanci a yanzu.” Sanata Sahabi Alhaji Ya’u, mai wakiltar Zamfara ta Arewa, ya yaba wa Matawalle bisa yadda yake wakiltar jihar a majalisar zartarwa, sannan ya gode wa Shugaba Tinubu bisa goyon bayan da yake baiwa jagororin APC daga Zamfara.
Sanata Tijjani Yahaya Kaura ya ce: “Zamfara jiha ce ta APC an haife ta a Zamfara!” Ya kira ga dukkan ’yan jam’iyya su yi aiki tare da zuciya ɗaya. Hon. Dr. Abdulmalik Zubairu ya yi addu’ar samun zaman lafiya a jihar, musamman ga waɗanda matsalolin tsaro ya shafa.
A ƙarshe, an yi kira ga haɗin kai, zaman lafiya, da ci gaba da goyon bayan gwamnatin Tinubu domin ayukkan alheri su ci gaba a Najeriya.









