Aƙalla mutane 41 ne suka mutu a wani harin sama da ake zargin sojoji ne suka kai a Kordofan da ke kudancin Sudan, kamar yadda shaidu da suka halarci jana’izar mamatan suka tabbatar, yayin da mayaƙan RSF da wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam suka ɗora alhakinsa kan gwamnatin ƙasar.
Mayaƙan RSF tare da masu mara musu baya a yankin Kordofan da ke kudancin Sudan, ƙarkashin jagorancin Abdelaziz Al-Hilu, sun zargi sojojin ƙasar da kai hari a ƙauyen Komo ranar Asabar ɗin da ta gabata.
Wata ƙungiyar kare hakkin ɗan Adam wadda ke tattara alƙaluman cin zarafi daga ɓangarorin biyu na yaƙin watanni 31 a Sudan, ta ce an kai harin jirgin saman a kan makarantar koyon aikin jinya da ke ƙauyen na Komo, inda ya laƙume rayukan ɗalibai da dama.
Tih Issa mazaunin ƙauyen Heiban ya tabbatar da cewa sun gina ƙaburbura sama da 40 na mutanen da suka mutu sanadiyar harin.
Sai dai duk da wancan zargi da akayi wa sajojin na Sudan, wata majiyar sojin ƙasar da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa dakarunta ba sa kai hari kan fararen hula ko gidajen su.
Tun a tsaƙiyar watan Afrilun 2023 ne yaki ya ɓarke a Sudan, tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da raba miliyoyi da muhallansu wanda ya haifar da matsalar ayyukan jinƙai mafi muni a duniya.








