Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami, ya ƙaryata zargin da Hukumar EFCC take masa cewa yana da haɗi asusun banki 46 ba bisa ka’ida ba.
A cewar mai magana da yawunsa, Bello Doka, Malami ba shi da alaƙa da marigayi shugaban kasa Janar Sani Abacha, kuma ba shi da hannu a kowane irin rashawar kuɗi kamar yadda EFCC ke zargi. Doka ya ce tsohon ministan yana da asusun banki guda shida da sunansa waɗanda hukumar ta sani, kuma duk wanda ke kusa da shi ya san su.
“EFCC ta san asusunsa shida da ke cikin sunansa; zargin alaƙa da asusun banki 46 ba bisa ka’ida ba abin ban dariya ne kuma labari ne marar tushe, kuma ya bayyane, tsohon ministan ba shi da hannu akan dawo da kuɗin Abacha,” in ji Doka.
Ya lura cewa hukumar ba ta sanar da tsohon ministan a hukumance game da zargin alaƙa da asusun banki 46 da ake zargi lokacin da aka kira shi don tambayoyi ba.
Ya ƙara da cewa hukumar ya kamata ta bayyana tare da janye zargi akan asusun banki 46, domin bayyana gaskiya da adalci, ya ce shiga kafofin watsa labarai game da batun na hukumar bai isa ya tabbatar da zarginsu ba.








