Home Labarai Gwamnatin Jihar Kano ta nemi a kama Ganduje da sanata Barau saboda...

Gwamnatin Jihar Kano ta nemi a kama Ganduje da sanata Barau saboda yunkurin kafa hukumar hisbah mai zaman kanta

212
0

Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta yi kira da a gaggauta bincike da kamo tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa kalamansa na nuni da tada tarzoma inji majalisar. “masu tayar da hankali” game da yanayin tsaro a jihar.

Wannan ya biyo bayan tattaunawa a taron majalisar zartarwa karo na 34 da aka gudanar a ranar Alhamis a fadar gwamnatin Kano, inda mambobin suka ce sun yi nazari kan kalaman da Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattijai Barau I. Jibrin suka yi a kwanan nan, suna zargin cewa Kano na fuskantar barazanar ‘yan bindiga kuma suna sanar da shirin daukar mutane 12,000 a cikin wata sabuwar kungiyar jami’ai ta addini da ake kira Khairul Nas.

A lokacin da yake bayyana wa ‘yan jarida sakamakon taron a ranar Juma’a, kwamishinan yada labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce wadannan yunƙurin da suke yi na kafa hukumar mai zaman kanta na iya cutar da yaƙi da tsaro da gwamnatoci ke yi.

Ya ƙara da cewa dole ne a bincike shi domin ba za mu iya kallon yadda zai rusa zaman lafiyarmu a jihar ba.” Gwamnatin jihar ta sake nanata godiyarta ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro saboda tallafin da suke bayarwa wajen yaki da rashin tsaro, kuma ta jaddada cewa ba za a bar kowa ko kungiya ta kafa ‘yan bindiga ba ta kowace hanyar ba.

Ta kuma yi kira ga masu mukamai da ‘yan siyasa da su daina fitar da kalaman da za su iya tayar da hankali, tare da tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, bin doka da oda a duk fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 8   +   5   =