Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (Police Service Commission), tare da haɗin gwiwar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, ta sanar da fara ɗaukar sabbin ‘yan sanda masu matsayin Constable guda 50,000, kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya Umarta.
Tsarin ɗaukar waɗannan ma’aikata, a cewar hukumar, ya biyo umarnin Shugaban ƙasa na ƙarfafa aikin ‘yan sanda da al’umma, inganta tsaro a cikin ƙasa, da ƙara yawan ma’aikata a cikin hukumar ‘yan sanda.
A ranar 26 ga Nuwamba, 2025, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci tsaro a faɗin ƙasar, inda ya umurci ‘Yan Sandan Najeriya da Sojoji su ɗauki ƙarin ma’aikata don magance tabarbarewar tsaro a ƙasar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban hukumar Torty Kalu ya fitar a ranar Alhamis, hukumar ta ce za a buɗe shafin yanar gizo domin neman gurbin daga ranar 15 ga Disamba, 2025, zuwa 25 ga Janairu, 2026.
Sanarwar ta ce: “Hukumar kula da Ayyukan ‘yan’sanda, tare da haɗin gwiwar Hukumar yan’sandan, ta sanar da zata fara ɗaukar sabbin ‘Yan Sanda Constable guda 50,000 a cikin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya umarta. Bisa wannan umarnin da shugaban ƙasa da nufin ƙarfafa aikin ‘yan sanda,
hukumar ta amince da buɗe shafin yanar gizo don karɓar takardun neman aiki daga ’yan Najeriya ga masu cancanta.
Matsayin General Duty, ana buƙatar masu nema su mallaki Shedar gama makaranta ta sakandare, da sakamakon jarabawar sakandare NECO ko WAEC tare da a ƙalla maki biyar darasai, ciki har da Turanci da Lissafi, kar ya zoma dalibi yayi zaman jarabawar sama da biyu.
Masu neman matsayin Jami’an na musamman (Specialists) zasu mallaki aƙalla maki huɗu na darasai, ciki har da Turanci da Lissafi, su ma a cikin zamanta kar su wuce fiye da sau biyu, kuma dole ne su sami aƙalla shekaru uku na ƙwarewa da takardar shaidar gwaji ta sana’a da ta dace.”
Ya ce masu nema dole ne su kasance ’yan ƙasar Najeriya ta haihuwa. “Masu neman General Duty dole ne sun kai shekaru 18 zuwa 25, yayin da masu neman jami’in na musamman (Specialists) su kai shekaru 18 zuwa 28. Masu neman General Duty ana buƙatar masu tsawon mita 1.67 ga maza da tsawon 1.64 ga mata.
Duk takardun neman aikin za a miƙa ta adireshin yanar gizo shafin da aka tsara,” in ji shi.








