A ranar 26 ga watan Nuwamba, an harbe sojojin Tsaro na Ƙasa (National Guard) biyu na Amurka a tsakiyar birnin Washington, D.C., nesa kaɗan da Fadar shugaban ƙasar. Hakan ya sa jami’an tsaro su yi gaggawar zuwa wajan da lamarin ya faru haka zalika, su rufe yankin na ɗan lokaci.
Harbin ya faru da misalin karfe 2:00 na rana a mahaɗar titin 17th Street NW da I Street NW, kusa da harabar shugaban. harbin ya rutsa da sojojin biyu, waɗanda ke cikin rukunin da aka tura birnin Washington inda har suka ji rauni.
Rahotannin farko sun tabbatar da cewa jami’an suna cikin wani yanayi mai tsanani, amma daga baya aka ji cewa duka biyu sun mutu.
An kama wani mutum ɗaya da ake zargi nan take bayan harbin, kuma shi ma ya ji rauni mai tsanani a lokacin musayar harbi.
An rufe Fadar White House na ɗan lokaci saboda yanayi na tsaron rai, an kuma killace wasu yankuna da ke kusa, ciki har da Farragut Square. Daraktan FBI Kash Patel ya zo wurin da abin ya faru don jagorantar ayyukan gwamnatin tarayya.

Wannan al’amari ya ƙara nuna damuwa game da hare-haren da ake kai wa jami’an tsaro da sojoji a babban birnin ƙasar, inda har takai da shugaban ƙasar Donald Trump ya wallafa wani hoto mai ɗauke da rubutun sa a kafar sada zumunta na twitter (x).
Trump ya bayyana cewa lallai dole ne a hukunta duk wanda aka samu da wannan laifin kuma zasu girbi abun da suka shuka.








