Home Labarai Za mu tsara kasafin kuɗin 2026 bisa buƙatun al’ummar Sokoto’ ~ Ahmad...

Za mu tsara kasafin kuɗin 2026 bisa buƙatun al’ummar Sokoto’ ~ Ahmad Aliyu

280
0

Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu ya ce gwamnatinsa za ta tsara kasafin kuɗin shekarar 2026 bisa buƙatun da al’ummar jihar suka gabatar.

Yayin da yake jawabi a wani taron tattaunawa kan kasafin kuɗin jihar na 2026, gwamnan jihar Ahmad Aliyu ya ce ingantaccen kasafin kuɗi shi ne wanda ya fito daga buƙatun jama’a, ba kawai daga teburin gwamnati ba.

“Mun zo nan ne domin sauraron ku, domin ku ne tushen abin da za mu tsara,” in ji Gwamnan.

Taron, ya ƙunshi manyan jami’an gwam­nati da shugabannin ƙananan hukumomi, masu ruwa da tsaki, ƙungiyoyin matasa, da na mata.

Gwamnatin jihar ta ce ta shirya taron ne da nufin shigar da ra’ayoyin al’umma cikin kasafin kuɗin 2026.

Gwamna Ahmad Aliyu ya ce kasafin na 2026 – da zai gabatar nan ba da jimawa ba – zai fi mayar da hankali kan ayyuka masu tasiri ga rayuwar al’umma.

Ahmad Aliyu ya ce kasafin kuɗin shekarar mai zuwa zai mayar da hankali ne kan manyan abubuwa guda huɗu da suka haɗa da bunƙasa tattalin arziki da gina abubuwan more rayuwa da kuma samar da tsaro da zaman lafiya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Prove your humanity: 9   +   2   =